Magana: , 1816.

Kidi: , 1867.


Daa, mala’iku ke shaidar
Haihuwar Yesu Mai Ceto.
Ji labarin farinciki
Wanda shi ke dominku.

Refrain

Zo, ku yi masa sujada
Shi Sarkin Sarakuna.

Makiyaya suna tsaron
Garkensu da daren nan.
Haske ne ya kewaye su,
Aka shaida musu ma.

Refrain

Masu hikima na duniya
Bar zurfin tunaninku
Nemi ceto wurin Yesu,
Kuna jin labarinsa.

Refrain

Sarakuna, talakawa
Malamai, almajirai
Mazaje da mata duka,
Tsofaffi da jarirai.

Refrain